Birane kamar su Abala Tanout Tahoua Zinder da Yamai na daga cikin irin wadanan wurare da sufetoci masu aikin bincike suka gano an handame daruruwan million cfa kamar yadda ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya bayyana
A daren jiya lahadi ne kungiyar ‘yan tawayen M23 mai gwagwarmaya da makamai da sojojin Rwanda suka kutsa kai zuwa tsakiyar birnin Goma bayan shafe makonni suna tunkararsa daga lardin Kivu na Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo.
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke huldar diflomasiyya da Rwanda yayin da ake gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda da dakarun gwamnatin a kusa da muhimmin birnin Goma na gabashin kasar.
Wani harin jirgi mara matuki a kan asibiti daya da ya rage yana aiki a El-Fasher a yankin Darfur na kasar Sudan, ya kashe mutane 30 kana ya jikata wasu da dama, a cewar wata majiyar kiwon lafiya a yau Asabar.
Za a soke bukatar neman iznin tafiye-tafiye ga ilahirin ‘yan Afrika, in banda ‘yan kasashen Somaliya da Libya, saboda dalilai na tsaro.
A wanan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar warware sabani da zuba jari da ake kira CIRDI inda yake neman a biyashi diyya dai dai da asarar da ya tafka a mahakar Uranium da ke arewacin Nijar
A cewar Ministan tsaron Nijar, an tanadi motoci da jirage da makaman yaki sannan hafsoshin kasashen uku na tattaunawa da juna kuma tuni suka kammala tsara yadda ayyukan rundunar za su gudana.
A wani al'amari mai matukar bakanta rai, arangamar da ta kaure tsakanin mahaka ma'adinai ba bisa ka'ida ba da jami'an tsaro a Ghana ta yi ajalin takwas daga cikinsu.
An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.
Jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar sun cafke tsohon ministan man fetur Barke Moustapha kwanaki kadan bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta ayyana shirin gudanar da bincike a matatar man hadin gwiwar China da kasar
Domin Kari
No media source currently available