Malakar kasa batu ne da ke yawan janyo takaddama a Afrika ta Kudu, inda farar fata ke ci gaba da mallake galibin gonakin kasar shekaru 30 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
Shugaban hukumar Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka Dr Omar Alieu Touray, ya sanar cewa ya sami wasikun bukatar tattaunawa daga kasashe 2 cikin mambobin kungiyar AES 3, duk da cewa tuni al’umomi da hukumomin kasashen suka yi bukin tabbatar da ficewarsu a hukumance.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kai farmakin a ranar Asabar a shafukan sada zumunta, yana mai bayyana lamarin da auna "Babban mai shirya kai hari na ISIS da sauran 'yan ta'addan da ya dauka kuma yake jagoranta."
Hukumomin lafiya a kasar Sudan sun sanar a ranar Asabar cewa, wani harin da wasu ‘yan bindiga da ke yaki da sojojin kasar suka kai wata budaddiyar kasuwa a birnin Omdurman na kasar Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 54 tare da jikkata wasu da dama.
A ranar Alhamis ne aka kwashe dakaru a sansanonin sojin Congo da ke lardin Bukavu don karfafa tsaro a wuraren da ke kan hanyar zuwa babban birnin lardin, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.
Uganda ta tabbatar da barkewar annobar Ebola a Kampala, babban birnin kasar, inda mutumin farko da aka tabbatar yana dauke da cutar ya mutu a jiya Laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana a yau Alhamis
A yau Laraba ne wani karamin jirgin sama dauke da ma’aikatan hakar mai a jihar Unity ta Sudan ta Kudu yayi hatsari tare da hallaka mutane 20, a cewar hukumomi
Sai dai, saboda tabbatar da hadin kan kasashen yankin, ECOWAS ta umarci mambobinta da su ci gaba da amincewa da fasgo din tafiye-tafiyen kasashen 3 da ke dauke da alamar kungiyar har sai abin da hali ya yi.
"Daga karshe za su yi nadama duk kasashen 3 ba su da iyaka da teku in za su shigo da kaya sai ta Benin, Senegal ko Najeriya.”
Umarnin Zartarwar shugaba Trump zai dakatar da bada tallafin abinci ga yaran da suke fama da matsalar rashin abinci a Habasha
Wani dan jarida da ke Goma, ya fada wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa ana ci gaba da artabu a yankin tashar jirgin sama da ke birnin sannan ya ce da alamu fadan na dada ta’azara.
A yau Talata MDD tace akwai matukar damuwa dangane da yanayin bada agaji a garin Goma na Jamhuriyar Congo da aka yiwa kawanya, ganin yawan mutanen da aka raba da muhallansu, ga karancin abinci da satar kayan agaji da ambaliya ga asibitoci na marasa lafiya da kuma yadda fyade ya zama ruwan dare
Domin Kari
No media source currently available