‘Yan kasar Afirka ta Kudu farar fata sun nuna goyon bayansu ga shugaba Donald Trump a yau Asabar, inda suka taru a ofishin jakadancin Amurka da ke Pretoria, inda suka yi ikirarin cewa gwamnatinsu ta nuna musu wariyar launin fata.
A ranar Asabar 15 ga watan Febrairu aka yi bikin bude babban taro na kasa a karkashin jagorancin shugaban gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar tare da halartar tsofaffin shugabannin kasar uku da sauran manyan baki da aka gayyato daga sassan kasar.
A ranar Juma’a ne ‘yan tawayen M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo suka shiga birnin Bukavu mafi girma na biyu a yankin, a cewar mazauna yankin da shugabannin kungiyoyin jama’a.
Yayin da Turai ke fadi tashin neman iskar gas da za ta maye gurbin ta Rasha, an sake farfado da shirin tura iskar gas din daga Najeriya zuwa Turai.
Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce za a yi tafiya da kowa a tattaunawar, wadda za ta tsara abubuwan da gwamnati za ta fi baiwa muhimmanci, sannan kuma za ta tsara jadawalin sauyin mulkin.
Fafatawar ta yau Talata na faruwa ne a kusa da garin Ihusi mai tazarar kilomita 70 daga babban birnin lardin Bukavu da kuma filin saukar jiragen saman yankin mai nisan kilomita 40.
Rikicin na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo yana kara muni ne bayan da kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kwace Goma, wani gari mai muhimmanci a lardin Kivu ta Arewa dake kudancin DR Congo.
Hukumomi sun ce sun kubutar da bakin haure 76 sannan sun tsare wani dan Libya da wasu ‘yan kasar waje 2 bisa tuhumar su da ake yi da tsarewa da kuma azabtar da bakin hauren.
Sam Nujoma, dan gwagwarmayar neman ‘yancin kai wanda ya jagoranci Namibia samun ‘yancin kai daga mulkin wariyar launin fata na Afrika ta Kudu a shekarar 1990, ya kuma yi shugaban kasar na tsawon shekaru 15 ya rasu. Yana da shekaru 95.
Jakadan jamhuriyar Benin a Nijar ya roki gafarar al'ummar jamhuriyar Nijar a madadin gwamnatin Patrice Talon da al'ummar kasar baki daya, dangane da sabanin da ya biyo bayan takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa a Nijar a shekerar 2023, a sanadiyar juyin mulkin da soja suka yi wa gwamantin farar hula.
Domin Kari
No media source currently available