Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan: MDD Ta Nuna Damuwa Kan Shirin RSF Na Kafa Hukumomi A Yankunan Da Ta Karbe


'Yan Sudan suna nuna goyon baya ga sojojin kasar a birnin Gedaref da ke gabashin kasar a ranar 22 ga watan Febrairun 2025.
'Yan Sudan suna nuna goyon baya ga sojojin kasar a birnin Gedaref da ke gabashin kasar a ranar 22 ga watan Febrairun 2025.

“Fiye da rabin al’ummar kasar – mutum miliyan 24.6 – na fuskantar yunwa mai tsanani. Ayyukan kiwon lafiya sun rushe gaba daya. Miliyoyin yara sun shiga rudani kuma an yanke su daga ilimi na hukuma.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna damuwa a ranar Laraba game da sanarwar da ‘yan sandan soja na Rapid Support Forces na Sudan suka yi a farkon makon nan cewa suna shirin kafa wata sabuwar hukuma mai mulki a yankunan da suke da iko a cikin kasar.

A gefe guda, Ofishin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar da rahotannin kisan gilla a yankunan da suka canja hannun iko, lamarin da ke kara tayar da hankula kan aikata manyan laifukan yaki.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma bayyana cewa "halin da ya riga ya zama mawuyaci" a Sudan ya ƙara muni tun bayan bayanin da aka gabatar a taron Majalisar Tsaro 'yan makonni da suka gabata, inda aka nuna cewa yunwa ta zama gaskiya a sassa da dama na ƙasar.

“Fiye da rabin al’ummar ƙasar – mutum miliyan 24.6 – na fuskantar yunwa mai tsanani. Ayyukan kiwon lafiya sun rushe gaba daya. Miliyoyin yara sun shiga ruɗani kuma an yanke su daga ilimi na hukuma.” In ji Edem Wosornu, Darektar Ayyuka da Kare Hakkin Jama’a a Ofishin Ayyukan ba da Agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA.)

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG