A tattaunawar ta yau Talata, Rasha ta Shaida wa Amurka cewa tana adawa da wata kasa mamba a kungiyar tsaron NATO ta aika da sojojinta a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta
Sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya dare kan teburi guda da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov da mashawarcin shugaban Amurka akan harkokin tsaro Mike Waltz da kuma jakadan Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya a gefensa.
Babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Marco Rubio, na ci gaba da fadi tashin cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa a Ukraine da Gabas Ta Tsakiya
An gano inda dukkanin fasinjoji da ma'aikatan jirgin suka shiga, kamar yadda tashar jiragen saman ta bayyana a sanarwar data wallafa a shafinta na X
Tattaunawar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata Trump ya tattauna da Putin ta wayar tarho tare da umartar manyan jami’ai su fara tattaunawa game da yakin, wanda ya sha nanata shan alwashin kawo karshensa a yakin neman zabensa.
Sojojin Ruwan Amurka da jiragen kasashe kawayenta irin su Canada, Birtaniya da Faransa sukan ratsa ta tekun Taiwan akalla a kowane wata. China wacce take ikirarin cewa Ruwan Taiwan yana cikin yankin ta, ta kuma sheda cewa hanyar ruwan ta musamman mallakin ta ne.
Hamas ta saki wasu karin mutane 3 a jiya Asabar a wata musayar da aka sako fursinonin Falasdinawa kusan 400, wanda aka sako da yammacin jiyan.
Kungiyar mayakan Hamas ta bayyana sunayen mutane 3 da take garkuwa da su wanda take shirin sake su a a yau Asabar, a musayar sako fursinonin Falasdinawa, wani yunkuri na bayan nan dake kunshe a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sa’o’i kadan kafin wannan lokaci, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana tsananin damuwa game da makomar mutanen da ake garkuwa dasu tsawon watanni 16 a zirin na Gaza.
Ga dukkan alamu takaddamar cinakayya a matakin kasa da kasa sai ma abin da ya yi gaba, saboda Trump ya ce babu gudu ba ja da baya.
Bayan da aka shiga fargabar yiwuwar a koma kazamin yaki a Gabas Ta Tsakiya saboda yiwuwar wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta, da alamar al'amura sun daidaitu a kalla a yanzu.
Lamarin ya faru ne yayin da mambobin kungiyar ma’aikata suke zanga-zanga.
Domin Kari
No media source currently available