Manyan jami’an diflomasiyar Amurka da Rasha sun gana a Saudiya a yau Talata, domin tattaunawa a kan yadda za su inganta alakarsu da ta yi tsami, tattaunawa irinta ta farko tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
Sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya dare kan teburi guda da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov da mashawarcin shugaban Amurka a kan harkokin tsaro Mike Waltz da kuma jakadan Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya, Mike Witkoff, a gefensa.
Lavrov ya samu rakiyar babban hadimin shugaban Rasha Yuri Ushakov.
Ministan wajen Saudiyya yarima Faisal Bin Farhan da mashawarcin sarkin kasar a kan harkokin tsaro Musaad Bin Muhammad Al-Aiban suma sun halarci tattaunawar.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yace ba’a gayyaci Kyiv zuwa tattaunawar ba.
A jiya Litinin shugabannin nahiyar Turai suka gana a birnin Paris domin tattaunawar gaggawa a kan yadda za su maida martani kan sauyin bazatan da sabuwar gwamnatin Trump ta zo da shi.
Dandalin Mu Tattauna