Jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ta Jamus ta lashe zaben kasa da aka gudanar a ranar Lahadi, amma kuri’ar da aka kada ta bai wa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta AfD sakamako mafi kyau a matsayi na biyu.
Al’ummar Jamus sun kada kuri'a a ranar Lahadi domin zabar sabuwar gwamnati a kasar.
Wadanda za a sakin sun hada da, mutane 445 daga zirin Gaza da aka kama bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin, 60 daga cikinsu na zaman gidan kaso na dogayen shekaru da 50 da aka yankewa daurin rai da rai, da 47 da aka sake kamawa bayan musayar fursunonin 2011
Gawarwakin Yahudawa 4 da ake garkuwa da su a Gaza sun koma Isra’ila a yau Alhamis a musayar fursunoni ta baya-bayan nan karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakanin Isra’ilar da kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas.
An fara murza gashin baki tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Zelenskyy kan makomar yakin Ukraine.
Marco Rubio, jiya Talata yace Amurka tana kokarin ganin an samu mafita adala mai dorewa wajen kawo karshen yakin da Rasha ta shafe kimanin shekaru uku ta na yi a Ukraine, sai dai dole ne Rashar da Ukraine, kowaccen su, ta hakura da wani abu, kafin a iya cimma zaman lafiya.
A tattaunawar ta yau Talata, Rasha ta Shaida wa Amurka cewa tana adawa da wata kasa mamba a kungiyar tsaron NATO ta aika da sojojinta a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta
Sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya dare kan teburi guda da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov da mashawarcin shugaban Amurka akan harkokin tsaro Mike Waltz da kuma jakadan Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya a gefensa.
Babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Marco Rubio, na ci gaba da fadi tashin cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa a Ukraine da Gabas Ta Tsakiya
An gano inda dukkanin fasinjoji da ma'aikatan jirgin suka shiga, kamar yadda tashar jiragen saman ta bayyana a sanarwar data wallafa a shafinta na X
Tattaunawar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata Trump ya tattauna da Putin ta wayar tarho tare da umartar manyan jami’ai su fara tattaunawa game da yakin, wanda ya sha nanata shan alwashin kawo karshensa a yakin neman zabensa.
Sojojin Ruwan Amurka da jiragen kasashe kawayenta irin su Canada, Birtaniya da Faransa sukan ratsa ta tekun Taiwan akalla a kowane wata. China wacce take ikirarin cewa Ruwan Taiwan yana cikin yankin ta, ta kuma sheda cewa hanyar ruwan ta musamman mallakin ta ne.
Domin Kari
No media source currently available