Hakan na nufin daga cikin wadanda ake garkuwa dasu 26, 18 ne kawai ke raye.
Shaidun gani da ido sun ce tawagar farko ta isa birnin Gaza sanyin safiya bayan da aka bude mashigar farko dake yankin tsakiyar gaza da misalin karfe 7 na safe agogon GMT. An sake bude wata mashigar bayan sa’o’i 3, inda aka kyale ababen hawa su wuce.
Sojojin Isira’ila sun bude wuta kan Falasdinawa a yankunan Lebanon da Gaza har su ka kashe mutane 23 baya ga wadanda su ka raunata.
Sojojin 4 mata na Isra'ila sun yi murmushi, tare da daga hannu da babban yatsa ga dimbin jama'ar da suka tattaru a wani dandalin Falasdinu a birnin Gaza. Hukumar gidan yarin Isra'ila ta sanar da cewa ta kammala sakin Falasdinawa 200.
Gwajin makaman da Pyongyang ta yi shi ne na farko tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House a ranar Litinin.
Hamas ta shirya ta saki wasu matan Isra’ilawa hudu da ake garkuwa dasu a yau Asabar a wata musaya da sakin fursinonin Falasdinawa a karo na biyu a karkashin Shirin tsagaita wuta a Gaza.
Shugabar kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala ta bukaci kasashe su kwantar da hankula akan batun haraji, inda tayi gargadin cewar yakin kasuwanci ba zai haifar da da mai ido ga tattalin arzikin duniya ba.
A wanan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar warware sabani da zuba jari da ake kira CIRDI inda yake neman a biyashi diyya dai dai da asarar da ya tafka a mahakar Uranium da ke arewacin Nijar
A zamanin wa’adinsa na farko, Trump ya yi amfani da manufar yin matsin lamba mai tsanani a kan Iran, inda ya janye Amurka daga shahararriyar yarjejeniyar nukiliyar nan ta 2015 wacce ta kakaba takunkumi a kan shirin nukiliyar Iran domin sassauta mata takunkuman.
Kamar yadda aka zaci zai faru, bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa ya tsaurara sharuddan zama dan kasa, 'yan jam'iyyar Democrats sun ce ba za ta sabu ba.
Biyu daga cikin wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin da suka duro daga benen don tsira da ransu.
Domin Kari
No media source currently available