Hamas da Isra’ila na daf da gudanar da musayar fursunoni a karo na 5 a gobe Asabar karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta 19 ga watan Janairu.
Matukin jirgin da fasinjansa mutum guda sun mutu a hatsarin, wanda ya faru jim kadan bayan da jirgin kirar King Air F90 ya tashi daga filin saukar jiragen sama na Campo de Marte, da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama a cikin kasar.
Kotun hukunta manyan laifuffukan kotu ce ta dindindin da ka iya gurfanar da daidaikun mutane a kan laifuffukan yaki da laifuffukan cin zarafin bil adama da aikata kisan kiyashi da kuma mamayar wani yankin na kasashe mambobin kotun daga wata kasa ko wasu mutane daga cikin al’ummar kasar.
A yau Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Isra’ila zata mikawa kasarsa iko da Gaza bayan lafawar rikici tare da tsugunar da al’ummar zirin a wani wuri na daban, abinda yace ba zai bukaci tura dakarun sojin Amurka zuwa yankin ba.
Ga dukkan alamu, yakin Janhuriyar Demokaradiyyar Congo na dada kazancewa duk da kokarin da ake na kira ga bangarorin da ke fadan.
Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.
Tun bayan hawansa kan karagar mulki a 2023, Melei ke takaicin yadda ake kashe kudaden gwamnati, bayan da ya sha alwashin tabbatar da ba’a samu gibi a kasafin kudin kasar ba bayan shafe shekaru ana wadaka.
A yau Laraba, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa game da shirin Shugaba Donald Trump mai rikitarwa na cewar Amurka za ta karbe iko da Zirin Gaza tare da sake tsugunar da al'ummarsa.
An tsara cewa galibin fursunonin za su tafi gudun hijira da zarar an sakesu, inda a Lahadin da ta gabata a birnin Doha, Fidan yace Turkiya na iya baiwa da dama daga cikinsu mafaka.
An mika wani ba-Faranshen Isra’ila Ofer Kelderon mai shekaru 54 da kuma Yarden Bibas mai shekaru 35 ga Red Cross a garin Khan Younis dake kudancin Gaza kafin suka koma Isra’ila.
An tsara cewar Isra’ila za ta saki fursunoni 110, ciki har da yara kanana 30, domin musayar Yahudawa 3 da aka saki a yau Alhamis, kamar yadda wata kungiya mai fafautuka a kan Falasdinawa fursunoni ta bayyana.
Domin Kari
No media source currently available