Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Kamfanin Delta Ya Yi Saukar Gaggawa A Filin Saukar Jiragen Saman Toronto


An gano inda dukkanin fasinjoji da ma'aikatan jirgin suka shiga, kamar yadda tashar jiragen saman ta bayyana a sanarwar data wallafa a shafinta na X

Wani jirgin saman kamfanin Delta ya rikito a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Pearson da ke birnin Toronto a yau Litinin, a cewar jami'ai, inda tashar talabijin ta CBC ta bada rahoton cewar jirgin ya tuntsura ne yayin sauka.

Tashoshin talabijin na CBC da CP 24 sun ba da rahoton cewar mutane 8 ne suka jikkata.

Tashar jiragen saman Pearson ta bayyana cewa tana sane da hatsarin da ya samu jirgin saman kamfanin Delta kirar DAL. N da ya taso daga Minneapolis kuma tawagogin agajin gaggawa na can na kai dauki.

An gano inda dukkanin fasinjoji da ma'aikatan jirgin suka shiga, kamar yadda tashar jiragen saman ta bayyana a sanarwar data wallafa a shafinta na X.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG