Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rubio Na Saudiyya Wajen Tattaunawa Kan Zaman Lafiya


Marco Rubio da Yarima Muhammad bin Salman
Marco Rubio da Yarima Muhammad bin Salman

Babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Marco Rubio, na ci gaba da fadi tashin cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa a Ukraine da Gabas Ta Tsakiya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marcco Rubio ya isa Saudiyya jiya Litini don tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isira’ila da Hamas da kuma makomar Zirin Gaza idan an kawo karshen yaki.

Sabon babban jami’in diflomasiyyar Amurka din ya gana da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan.

Gabanin lokacin, an zaci tattaunawar ta su za ta raja’a ne kan kiran da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na cewa Falasdinawa masu yawan miliyan 2.3 su kaura daga Gaza zuwa kasashe makwabta, inda ita kuma Amurka za ta sake gina dan matsattsen zirin da ke daura da Kogin Meditareniya ta kuma mallake shi.

Kasashen Larabawa dai, ciki har da Saudiyya, sun yi watsi da shirin na Trump, kuma sun ci gaba da goyon bayan batun kirkiro kasar Falasdinu, wadda ta hada da Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG