A yau Talata, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya caccaki tattaunawar da jami’an Amurka da Rasha ke yi a saudiya, inda ya bayyanata tattaunawa akan yakin Ukraine ba tare da gudunmowar Ukraine din ba.
“Ana tattaunawa tsakanin wakilan Rasha dana Amurka akan Ukraine kuma babu Ukraine din,” kamar yadda Zelensky ya bayyana yayin ziyarar aikin daya kai Turkiya.
A tattaunawar ta yau Talata, Rasha ta Shaida wa Amurka cewa tana adawa da wata kasa mamba a kungiyar tsaron NATO ta aika da sojojinta a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda ministan harkokin wajen Moscow ya bayyana.
“Bayyanar dakarun soji daga wadannan kasashen nato, ko karkashin tutar wata kasar ketare ko ta tarayyar Turai koma ta kasashensu, ba zai sauya komai ba game da hakan.
“Tabbas, hakan abu ne da ba zamu amince da shi ba,” kamar yadda Sergei Lavrov ya shaidawa manema labarai yayin tattaunawar dake gudana a Saudiyya.
Dandalin Mu Tattauna