Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Ta Karbi Sunayen Mutum 3 Da Za’a Saki Gobe


Dakarun Isra'ila (Hoto: AP)
Dakarun Isra'ila (Hoto: AP)

Sa’o’i kadan kafin wannan lokaci, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana tsananin damuwa game da makomar mutanen da ake garkuwa dasu tsawon watanni 16 a zirin na Gaza.

A yau Juma’a, Isra’ila ta sanar da cewa ta karbi bayyanan mutane 3 da ake garkuwa dasu a zirin Gaza da za’a saki a gobe Asabar, a cewar jadawalin da aka tsara a yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan kwanaki da dama na rashin tabbas da musayar barazana da kungiyar Hamas.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan ta ba da tabbacin cewa za’a saki Isra’ilawa 3, da ya daga cikinsu na hannun kawarta “Islamic Jihad”, a karo na 6 na musayar Falasdinawa fursunoni tun bayan tsagaita wutar da aka yi a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata.

Mutane 3 sun hada, Sasha Trupanov, Bayahudan Rasha da Sagui Dekel-Chen, Bayahudan Amurka da kuma Yair Horn, Bayahude dan Argentina, a cewar ofishin Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Sa’o’i kadan kafin wannan lokaci, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana tsananin damuwa game da makomar mutanen da ake garkuwa dasu tsawon watanni 16 a zirin na Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG