A yau Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Isra’ila zata mikawa kasarsa iko da Gaza bayan lafawar rikici tare da tsugunar da al’ummar zirin a wani wuri na daban, abinda yace ba zai bukaci tura dakarun sojin Amurka zuwa yankin ba.
Ga dukkan alamu, yakin Janhuriyar Demokaradiyyar Congo na dada kazancewa duk da kokarin da ake na kira ga bangarorin da ke fadan.
Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.
Tun bayan hawansa kan karagar mulki a 2023, Melei ke takaicin yadda ake kashe kudaden gwamnati, bayan da ya sha alwashin tabbatar da ba’a samu gibi a kasafin kudin kasar ba bayan shafe shekaru ana wadaka.
A yau Laraba, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa game da shirin Shugaba Donald Trump mai rikitarwa na cewar Amurka za ta karbe iko da Zirin Gaza tare da sake tsugunar da al'ummarsa.
An tsara cewa galibin fursunonin za su tafi gudun hijira da zarar an sakesu, inda a Lahadin da ta gabata a birnin Doha, Fidan yace Turkiya na iya baiwa da dama daga cikinsu mafaka.
An mika wani ba-Faranshen Isra’ila Ofer Kelderon mai shekaru 54 da kuma Yarden Bibas mai shekaru 35 ga Red Cross a garin Khan Younis dake kudancin Gaza kafin suka koma Isra’ila.
An tsara cewar Isra’ila za ta saki fursunoni 110, ciki har da yara kanana 30, domin musayar Yahudawa 3 da aka saki a yau Alhamis, kamar yadda wata kungiya mai fafautuka a kan Falasdinawa fursunoni ta bayyana.
Dangi na jini sun hallaka kimanin mata 1000 a Pakistan a bisa hujjar cewar suna kokarin kare mutuncin iyalinsu ne, a cewar hukumar kare hakkin ‘yan adam ta Pakistan (HRCP).
Wata majiyar Hamas ta shaidawa AFP cewar kungiyar na tattaunawa da masu shiga tsakani domin matsa wa Isra’ila lamba ta saki fursunoni 110 da ya kamata a saki a yau Alhamis.
Bayan da Amurka ta nuna cewa za ta janye wasu daga cikin kudaden tallafin da ta ke bayarwa a bangarori daban daban na harkokin duniya, tuni aka shiga kokawa.
Domin Kari
No media source currently available