Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Ambato Sunayen Mutane 3 Da Zata Sake Su Yau Asabar


Wasu da aka sako a baya
Wasu da aka sako a baya

Kungiyar mayakan Hamas ta bayyana sunayen mutane 3 da take garkuwa da su wanda take shirin sake su a a yau Asabar, a musayar sako fursinonin Falasdinawa, wani yunkuri na bayan nan dake kunshe a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kamar yanda Hamas ta bayyana kana hukumomin Isra’ila sauka tabbatar, mutanen sun hada ne da ba-Amurke dan Isra’ila Sagui Dekel Chen mai shekaru 36 mazaunin Kibbutz Nir Oz a kudancin Isra’ila.

Rahoto ya nuna cewa an kama shi ne yayin da ya yi artabu da mayakan Hamas, a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoba 2023 da kungiyar ta kai a kudancin Isra’ila. Wata biyu bayan kama shi matarsa Avital ta haifi ‘yar su ta uku.

A cikin mutanen da za a saken akwai ba-Isra’ile dan Rasha Sasha Troufanov, mai shekaru 29 daga Kibbutz Nir Oz. Shima an kama shi ne yayin harin tare da mahaifiyarsa Yelena, da kakarsa Irina Tati da kuma budurwarsa Sapir Cohen. An sako matan uku duka a wata yarjejeniya a watan da ya gabata.

An kashe mahaifinsa Vitaly a cikin harin. Iyalan nashi sun koma Isra’ila ne daga Rasha shekaru 25 da suka gabata.

Mutum na ukun an bayyana sunansa da Lair Horn, ba-Isra’ilen Argentina daga Kibbutz Nir Oz. Hamas ta yi garkuwa da shi a cikin harinta, tare da dan uwansa Eitan, wanda bai samu shiga cikin yarjejeniyar ta yanzu ba.

Shirin sakin wadanda ake garkuwa da sun ya fada cikin rashin tabbas bayan da Hamas ta zargi Isra’ila da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, kana ta yi barazanar sake komawa ga yakin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG