Kungiyar mayakan Hamas ta bayyana kudurinta na mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila a jiya alkhamis, yayin da masu sulhu suke aiki tukuru don ganin an ci gaba da hana fada a daidai lokacin da ake zargin karya sharuddan yarjejeniyar da barazanar sake ci gaba da yaki.
“Bama ma fatan yarjejeniyar tsagaita wutar ta rushe a yankin zirrin Gaza, sannan muna da muradin ganin an aiwatar da ita da kuma tabbatar da cewa Isra’ila dake mamayar ita ma ta amince ga baki daya,” inji Abdel-Latif Al-Qanoua, mai Magana da yawun Hamas.
Qanoua ya kuma yi sukar abin da ya ayyana da “kalaman barazana da tsoratarwa” da Firan Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu da shugaban Amurka Donald Triump suka furta, y ana mai cewa, basa taimakama kiyaye sharudan yarjejeniyar tsagaita wutar.
A farkon makon nan, Hamas ta zargi Isra’ila da saba yarjejeniyar tsagaita wutar inda ta ci gaba da kai wa a’ummar Gaza harin sama sannan ta hana shigar da tallafin jinkai.
Dandalin Mu Tattauna