Sa’o’i kadan kafin wannan lokaci, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana tsananin damuwa game da makomar mutanen da ake garkuwa dasu tsawon watanni 16 a zirin na Gaza.
Ga dukkan alamu takaddamar cinakayya a matakin kasa da kasa sai ma abin da ya yi gaba, saboda Trump ya ce babu gudu ba ja da baya.
Bayan da aka shiga fargabar yiwuwar a koma kazamin yaki a Gabas Ta Tsakiya saboda yiwuwar wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta, da alamar al'amura sun daidaitu a kalla a yanzu.
Lamarin ya faru ne yayin da mambobin kungiyar ma’aikata suke zanga-zanga.
A farkon makon nan Hamas ta zargi Isra’ila da keta matsayar ta hanyar ci gaba da kai hare-haren sama a yankin na Gaza hade da hana shigar da kayayyakin agaji.
Matakin na Trump ya baiwa kawayensa na Turai mamaki-inda da dama daga cikinsu suka fito fili suna tuhumar hikimar hakan.
Fadar Kremlin ta bayyana cewa an shafe sa’a daya da rabi ana hira ta wayar tarho kuma Putin da Trump sun amince cewa lokaci ya yi da za su yi aiki tare
Yayin da Turai ke fadi tashin neman iskar gas da za ta maye gurbin ta Rasha, an sake farfado da shirin tura iskar gas din daga Najeriya zuwa Turai.
Kasashen Jordan da Masar, wuraren da Trump ya bada shawarar mayar da al’ummar Gaza fiye da miliyan 2, sun bayyana adawarsu da shirin, wanda ya kunshi karbe iko da yankin Falasdinawan da yaki ya daidaita, a jiya Talata.
"Rundunar soji za ta koma yaki mai tsanani, har sai an yi galaba kan Hamas," in ji Netanyahu a wani faifan bidiyo jiya Talata.
Vance ya kuma caccaki China a matsayin daya daga cikin “gwamnatocin kama karya” da dama ke nazarin yin amfani da kirkirarriyar fasaha wajen sarrafa al’ummarta a cikin gida da kuma wasu kasashen ketare.
Domin Kari
No media source currently available