Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rubio Ya Isa Saudiyya Gabanin Tattaunawar Rasha Kan Kawo Karshen Yakin Ukraine


Tattaunawar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata Trump ya tattauna da Putin ta wayar tarho tare da umartar manyan jami’ai su fara tattaunawa game da yakin, wanda ya sha nanata shan alwashin kawo karshensa a yakin neman zabensa.

Rasha ta bayyana cewar ministan harkokin wajenta Sergei Lavrov zai tattauna da manyan jami’an Amurka, ciki harda sakataren waje Marco Rubio, a gobe Talata, inda zasu maida hankali a kan kawo karshen yakin Ukraine tare da dawo da fafaffadar alaka tsakanin Rasha da Amurka.

A Litinin din nan, Rubio ya isa babban birnin Saudiyya, Riyadh, a tafiyar da aka tsara tunda fari cewa mashawarcin shugaban Amurka a kan harkokin tsaro Mike Waltz da jakada Steve Witkoff za su iso yau da yamma, inda za su hadu da shi a tattaunawarsa da Lavrov.

Tattaunawar za ta kasance cikin irinta na farko, da za’a yi ido na ganin ido tsakanin jami’an Rasha da Amurka a cikin shekaru da dama kuma manufarta ita ce share fagen ganawa tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewar Lavrov da Yuri Ushakov, kashawarcin Putin a kan manufofin kasashen ketare, zasu tashi zuwa Riyadh a yau Litinin.

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Tammy Bruce ya tabbatar da cewa Rubio da Waltz da Witkoff za su gana da tawagar Rasha a birnin Riyadh a gobe Talata.

Tattaunawar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata Trump ya tattauna da Putin ta wayar tarho tare da umartar manyan jami’ai su fara tattaunawa game da yakin, wanda ya sha nanata shan alwashin kawo karshensa a yakin neman zabensa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG