Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Soki Lamirin Jirgin Yakin Ruwan Canada Da Ya Ratsa Tekun Taiwan  


Printed Chinese and Canada flags are seen in this illustration, July 21, 2022
Printed Chinese and Canada flags are seen in this illustration, July 21, 2022

Sojojin Ruwan Amurka da jiragen kasashe kawayenta irin su Canada, Birtaniya da Faransa sukan ratsa ta tekun Taiwan akalla a kowane wata. China wacce take ikirarin cewa Ruwan Taiwan yana cikin yankin ta, ta kuma sheda cewa hanyar ruwan ta musamman mallakin ta ne.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Yau Litinin, sojin kasar China sun soki jirgin ruwan yakin Canada da ya ratsa Ruwan Taiwan, sannan sun ce dakarun su na sama da na ruwa ne suka sa ido sannan sun yiwa jirgin gargadi, a wani aiki da suka yi ‘yan kwanakin bayan da wani jirgin sojin Ruwan Amurka ya yi wani abu makamancin wannan.

Sojojin Ruwan Amurka da jiragen kasashe kawayenta irin su Canada, Birtaniya da Faransa sukan ratsa ta wannan hanyar akalla a kowane wata. China wacce take ikirarin cewa Ruwan Taiwan yana cikin yankin ta, ta kuma sheda cewa hanyar ruwan ta musamman mallakin ta ne.

Cikin wata sanarwa, kwamandan shiyyar gabas na sojojin China ya ce “da gangan Canada ta aikata hakan da zummar ta tada fitina sannan kuma tana neman rusa zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.

Sanarwar ta kara da cewa, “dakarun rundunar suna kasancewa cikin Shirin ko ta kwana a duk lokaci sannan a shirye suke su tunkari duk wata barazana da wata takala,”.

Sojojin Canada sun ki cewa uffan nan take.

Dukkanin gwamnatocin China da Taiwan sun tabbatar da cewa jirgin Ottawa ne.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG