Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Musayar Fursinoni Tsakanin Isra'ila Da Kungiyar Hamas Ta Falasdinawa


Israel Palestinians
Israel Palestinians

Hamas ta saki wasu karin mutane 3 a jiya Asabar a wata musayar da aka sako fursinonin Falasdinawa kusan 400, wanda aka sako da yammacin jiyan.

Da yammacin jiya Asabar din, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya isa Isra’ila domin fara rangadinsa na farko a yankin Gabas ta Tsakiya. Zai yi tattaunawa a kan shirin tsagaita wuta mai tattare da rudani da kuma shirin shugaba Donald Trump a kan Gaza a ganawarsa da da Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a yau Lahadi.

Mutanen ukun da aka sake a jiya Asabar dukkan su mazauna yankin Kibbutz Nir Oz ne dake kudancin Isra’ila.

An kama ba-Amurke dan Isra’ila Sagui Dekel Chen mai shekaru 36 mazaunin Kibbutz Nir Oz a kudancin Isra’ila yayin da ya yi artabu da mayakan Hamas, a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoba 2023 da kungiyar ta kai a kudancin Isra’ila. Wata biyu bayan kama shi matarsa Avital ta haifi ‘yar su ta uku.

An kuma sake ba-Isra’ile dan Rasha Sasha Troufanov, mai shekaru 29 daga Kibbutz Nir Oz. Shima an kama shi ne yayin harin tare da mahaifiyarsa Yelena, da kakarsa Irina Tati da kuma budurwarsa Sapir Cohen. An sako matan uku duka a wata yarjejeniya a watan da ya gabata. An kashe mahaifinsa Vitaly a cikin harin. Iyalan nashi sun koma Isra’ila ne daga Rasha shekaru 25 da suka gabata.

Mutum na uku an bayyana sunansa Lair Horn, ba-Isra’ilen Argentina daga Kibbutz Nir Oz. Hamas ta yi garkuwa da shi a cikin harinta, tare da dan uwansa Eitan, wanda ba shi cikin fuskar yarjejeniyar ta yanzu.

An mika mutanen ukun duka ga kungiyar Red Cross ta kasa da kasa a birnin Khan Younis dake Gaza kafin aka kwashe su zuwa ga sojojin Isra’ila.

A Tel Aviv, ‘yan uwa da abokan arziki sun kalli bidiyon sako mutanen yayin da ake shewa kana mutanen suka sauko cikin mota a inda aka mika su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG