An mika wani ba-Faranshen Isra’ila Ofer Kelderon mai shekaru 54 da kuma Yarden Bibas mai shekaru 35 ga Red Cross a garin Khan Younis dake kudancin Gaza kafin suka koma Isra’ila.
An tsara cewar Isra’ila za ta saki fursunoni 110, ciki har da yara kanana 30, domin musayar Yahudawa 3 da aka saki a yau Alhamis, kamar yadda wata kungiya mai fafautuka a kan Falasdinawa fursunoni ta bayyana.
Dangi na jini sun hallaka kimanin mata 1000 a Pakistan a bisa hujjar cewar suna kokarin kare mutuncin iyalinsu ne, a cewar hukumar kare hakkin ‘yan adam ta Pakistan (HRCP).
Wata majiyar Hamas ta shaidawa AFP cewar kungiyar na tattaunawa da masu shiga tsakani domin matsa wa Isra’ila lamba ta saki fursunoni 110 da ya kamata a saki a yau Alhamis.
Bayan da Amurka ta nuna cewa za ta janye wasu daga cikin kudaden tallafin da ta ke bayarwa a bangarori daban daban na harkokin duniya, tuni aka shiga kokawa.
Turmutsutsin da ya afku da goshin asubahi a bikin bautar kogin maha Kumbh Mela mai tsarki dake arewacin indiya ya hallaka gomman mutane a yau Laraba
Jirgin ruwan mallakin kasar Turkiya, na makare da tan 871 na kayan agajin da suka hada da janaretoci 300 da bandakunan tafi da gidanka 20, da tantuna 10, 460 da kuma barguna 14, 350, a cewar wani jami’in Turkiya.
Hakan na nufin daga cikin wadanda ake garkuwa dasu 26, 18 ne kawai ke raye.
Shaidun gani da ido sun ce tawagar farko ta isa birnin Gaza sanyin safiya bayan da aka bude mashigar farko dake yankin tsakiyar gaza da misalin karfe 7 na safe agogon GMT. An sake bude wata mashigar bayan sa’o’i 3, inda aka kyale ababen hawa su wuce.
Sojojin Isira’ila sun bude wuta kan Falasdinawa a yankunan Lebanon da Gaza har su ka kashe mutane 23 baya ga wadanda su ka raunata.
Sojojin 4 mata na Isra'ila sun yi murmushi, tare da daga hannu da babban yatsa ga dimbin jama'ar da suka tattaru a wani dandalin Falasdinu a birnin Gaza. Hukumar gidan yarin Isra'ila ta sanar da cewa ta kammala sakin Falasdinawa 200.
Domin Kari
No media source currently available