Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mota Ta Afka Cikin Jama’a, Tare Da Jikkata Mutane 28 a Jamus


Lamarin ya faru ne yayin da mambobin kungiyar ma’aikata suke zanga-zanga.

Wata mota da ta kutsa cikin taron jama’a a birnin Munich na kasar Jamus a yau Alhamis ta jikkata mutum 28.

‘Yan sanda sun ce ana tsare da direban motar kuma a lokacin da ake yunkurin kama shi sai da aka harbi motar.

Hukumomi sun ce direban mai shekaru 24 dan asalin Afghanistan ne da ke neman mafaka a kasar ta Jamus.

Lamarin ya faru ne yayin da mambobin kungiyar ma’aikata suke zanga-zanga.

Kakakin ‘yan sandan birnin Munich, Thomas Schelshorn, yace, “Da misalin karfe 10:30 ne wata mota ta kutsa cikin jama’a, kuma mutane da dama sun ji Rauni.

Gwamnan jihar Bavaria Markus Soder, ya fadawa manema labarai cewa akwai alamu da ke nuna cewa hari ne direban ya kai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG