Duk da nasarar da jami'an sojin Najeriya ke samu a yaki da 'yan bindiga a Najeriya, har yanzu a wasu yankuna mutane na fuskantar ayyukan 'yan bindigar.
Ko a jiya Alhamis 'yan bindiga sun yi garkuwa da masallata hadi da liman lokacin da suke sallar asubahi cikin masallaci a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Yankin Sabon Birni dake gabashin Sakkwato na daga cikin yankunan da matsalar rashin tsaro ta yi kaka-gida a arewa maso yammacin Najeriya, kuma yanzu haka yana daga cikin wuraren da sojoji ke fada da 'yan bindiga kamar yadda babban kumandan yanki na takwas na rundunar soji dake da hedikwata a Sakkwato, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya tabbatar.
"Yace yanzu haka suna kai farmaki babu kyakkyabtawa a Sabon Birni da Isa kuma sun tarwatsa sansanonin 'yan bindiga da yawa, suna samun galaba musamman tare da hadin guiwar aikin da suke yi da sojin sama"
To sai dai hakan bai hana 'yan bindiga samun sa'a suna mamayar mutane ba suna cin zarafinsu, tamkar dai yadda suka saba a baya.
Abin da ke kara tabbatar da hakan shi ne, harin da 'yan bindiga suka kai a garin Baushe dake gabashin Sabon Birni, inda suka tarar da jama'a na salla a masallaci suka kai musu farmaki, kamar yadda wani mutumin yankin na Sabon Birni ya tabbatar.
Shi ma dan majalisar dokoki na jiha wanda ke wakiltar jama'ar, Sa'idu Ibrahim, ya ce lallai an kai hari kuma an dauki masallata.
Sai dai acewar dan majalisar, lokacin da maharan suka je garin, yayin kokarin kama masallatan, sojojin da ke Taka-tsaba suka ji hayaniya ta yi yawa suka yunkura su kawo dauki, abinda ya sa barayin suka gudu da mutane goma, yayin da sauran jama'a suka samu tsira.
Mutanen yakin sun bayyana cewa wannan fada da sojoji ke yi da 'yan bindigar tamkar kara rura wutar ta'addacin 'yan bindigar ne a wasu wurare.
Dama dai mazauna yankunan da ke fama da matsalolin na rashin tsaro da masu sharhi a kan lamuran tsaro sun jima suna bayar da shawarwari cewa idan ana fada da 'yan bindiga a rika dagewa, kar a ja baya a bar baya da kura, kamar abinda ke faruwa yanzu a wasu yankunan arewacin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna