Fasatattun daliban jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo sun gudanar da zanga-zanga akan rashin hasken lantarki na kwanaki 100 a asibitin koyarwa na makarantar.
Asibitin dai shi ne inda daliban da ke nazarin fannin likitanci ke samon horo.
Tun a bara asibitin ke fama da daukewar wutar lantarki sakamakon basussukan da kamfanin rarraba hasken lantarki na Ibadan (IBEDC) ke bin sa.
A jawabinsa ga manema labarai, shugaban kungiyar daliban jami’ar badun, Kwamred Bolaji Aweda, ya bayyana daukewar lantarkin da matsalar data ki ci taki cinyewa, inda yace ta kassara harkar koyo da koyarwa a asibitin dama jami’ar baki daya.
Ya kara da cewar, dalibai sun kasa nazari yadda ya dace, sakamakon shafe kwanaki 100 ana fama da matsalar.
Aweda ya ci gaba da cewar daukewar lantarkin nuna iko ne tsakanin hukumomin kamfanin rarraba lantarki na ibedc dana asibitn koyarwar.
Dandalin Mu Tattauna