Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Na Ganawar Sirri Da Obasanjo

Tsohon Hoton Obasanjo (Hagu) da Atiku (dama)
Tsohon Hoton Obasanjo (Hagu) da Atiku (dama)

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke da Sanata Aminu Tambuwal wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto.

A yau Litinin tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya jagoranci wata tawaga domin ganawa da tsohon ubangidansa, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a gidansu da ke birnin Abeokuta, fadar gwamnatin jihar Ogun.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke da Sanata Aminu Tambuwal wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto.

Har sa'ilin hada wannan rahoto ba'a san ajandar taron ba saidai yana zuwa ne a daidai lokacin da 'yan siyasar da ke bangaren adawa ke tsare-tsaren lashe zaben shugaban kasar a shekarar 2027.

Atiku ya kasance mataimaki ga Obasanjo daga watan Mayun 1997 zuwa Mayun 2007.

Atiku da ya kasance dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya zo a mataki na 2 bayan Shugaba Bola Tinubu wanda ya lashe zaben.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG