An sanya Najeriya a mataki na 140 daga cikin kasashen duniya 180 a mizanin auna rashawa na 2024, a cewar rahoton kungiyar Transparency International (TI) mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya.
Rahoton da kungiyar ta (TI) ta saki a yau Talata ya nuna yadda matakin Najeriya ya karu da maki 5 idan aka kwatanta da rahoton 2023 sannan da maki 10 idan aka kwatanta da rahoton 2022.
Denmark ce kasa mafi karancin cin hanci da rashawa da maki 90 sai ‘yar uwarta Finland da ita ke yankin arewacin duniya wacce tazo ta 2 da maki 88, sannan kasar Singapore data zo ta 3 da maki 84.
Saidai, kasashe dake cikin rukunin mafi cin hanci da rashawa a fadin duniya sun hada da Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Venezuela.
An lura da cewar babu ko kasar afrika guda data shiga rukunin kasashe 10 mafi karancin cin hanci da rashawa da kasashen Turai suka mamaye.
A bisa la’akari da rahoton, kasashen Uganda da Madagascar da Iraki da Kamaru sun yi tarayya da iya a mataki daya inda dukkaninsu suka samu jumlar maki 26.
A saurari hiran Wakilin Muryar Amurka, Sarfilu Hashim Gumel da Shugaban hukumar Transparency International, reshen najeriya, Auwal Musa Rafsanjani kan rahoton:
Dandalin Mu Tattauna