Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ba da shawarar zartar da hukuncin kisa akan masu fataucin kwaya.
A cewar babbar daraktar hukumar, Mojisola Adeyeye, tsattsauran hukunci ne kawai zai dakatar da fataken kwaya musamman ma yadda take sanadiyar mutuwar kananan yara.
Shugabar hukumar ta NAFDAC ta kuma nemi hadin kan bangaren shari’a da majalisar kasa wajen ganin wannan buri ya zama gaskiya.
A cewarta, a shirye hukumar take ta yi hadin gwiwa da ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki a kan batun, inda Adeyeye ta koka da karancin ma’aikata a hukumar.
Ta yi amannar cewar da ma’aikata kimanin 2, 000 a fadin Najeriya da karancin kudade, babu yadda za’a yi NAFDAC ta gudanar da ayyukanta yadda ya dace.
Dandalin Mu Tattauna