Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ba Da Shawarar Mayar Da Ilimi A Matakin Farko Shekaru 12


Yara a makaranta
Yara a makaranta

Za’a tattauna da masu ruwa da tsaki yayin taron kwamitin ilimi na kasar da zai gudana a watan Oktoban bana kafin yanke shawara ta karshe game da tayin.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gabatar da tayin mayar da tsarin ilimi a matakin farko zuwa shekaru 12 sai dai ta musanta batun soke tsarin karamar sakandare (JSS) da babbar sakandare (SSS).

Sanarwar da daraktar yada labarai a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folashade Boriowo, ta fitar ce ta tabbatar da hakan.

A cewar Boriowo, minstan ilimi Tunji Alausa ne ya bayyana hakan yayin wani taron kwamitin ilimi na kasa (NEC) na musamman da ya gudana a Abuja a jiya Alhamis inda ya gabatar da shawarar domin tafka muhawara akanta-ba wai sauyin manufa ba ce ta nan take.

“An ja hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya game da wani rahoton bogi da ke nuni da cewa gwamnatin tarayya ta soke tsarin karama da babbar sakandare tare da maye gurbinsu da sabon tsarin ilimi a matakin farko na shekaru 12 ba tare da tsaiko ba. Muna son mu bayyana da babbar murya cewar hakan ba gaskiya ba ne,” kamar yadda sanarwar da aka fitar a yau Juma’a ta bayyana.

“Manufar shawarar ita ce komawa kan tsarin shekaru 12 na neman ilimi dole yayin da za’a cigaba da amfani da tsarin 6-3-3,” a cewar ma’aikatar ilimin.

Ma’aikatar ta kara da cewa za’a tattauna da masu ruwa da tsaki yayin taron kwamitin ilimi na kasar da zai gudana a watan Oktoban bana kafin yanke shawara ta karshe game da tayin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG