Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MTN Ya Kara Kudin Sayen Data A Najeriya


Nigeria MTN Fine
Nigeria MTN Fine

Karin wani bangare na karin kaso 50 cikin 100 na harajin kiran waya da sayen data, da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da shi saboda halin da kasuwa ke ciki a halin yanzu.

Kamfanin MTN na Najeriya ya kara farashin tsarin sayen gigabyte 15 na data a kowane mako zuwa Naira 6, 000 daga 2, 000.

Karin wani bangare na karin kaso 50 cikin 100 na harajin kiran waya da sayen data, da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da shi saboda halin da kasuwa ke ciki a halin yanzu.

Kamfanin ya tabbatar da sauyin, inda yace anyi hakan ne da nufin inganta ayyuka ga abokan huldarsa.

“Yello! muna neman gafara game da jinkiri mayar da martani da kuma matsalolin da aka fuskanta. Muna sanarda ku cewar a samu sauyi a baya-bayan na game da sauya tsarin haraji da nufin inganta ayyukan mu, sakamakon hakan kuke ganin sauye-sauyen aka manhajarmu. Muna takaicin duk rashin jin dadin da hakan zai haifar,” kamar yadda kamfanin ya wallafa a shafinsa na X.

Sabon tsarin farashin ya haifar da gagarumin tashin gwauron zabo a sauran tsare-tsaren sayen data suma. Misali, tsarin sayen terabyte 1.5 na data ya tashi daga Naira 150, 000 zuwa 240, 000 sannan tsarin sayen gigabyte 600 ya koma Naira 120, 000 daga 75, 000.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG