Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ilahirin ministocin gwamnatinsa dasu gaggauta bada bahasi akan ayyuka da nasarorin da suka samu ga al’ummar Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris, ne ya sanar da umarnin yayin ganawa da manema labarai a Abuja a yau Talata.
Idris ya bayyana cewar manufar bada bahasin ita ce sanar da ‘yan Najeriya game da cigaba da manufofin gwamnatin, tare da baiwa al’ummar kasa damar yin tambayoyi da kuma tattaunawa kai tsaye da ministtocin.
A halin yanzu Najeriya nada ministoci 48, adadi mafi girma a tarihin kasar.
Dandalin Mu Tattauna