Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware Naira bilyan 100 a kasafin kudinta na bana dake jiran Majalisar Dokokin kasar ta zartar dashi wajen samarda kananan turakun lantarki masu amfani da hasken rana a wasu zababbun manyan makarantu da jami’o’in tarayyar kasar da kuma asibitocin koyarwarsu.
Babban daraktan hukumar samar da lantarki a karkara (REA), Abba Aliyu, yace da zarar Shugaba Bola Tinubu ya zartar da kasafin kudin zuwa doka, hukumarsa za ta fara aikin samar da lantarki a makarantun gwamnatin.
Aliyu, wanda ya kasance bako a shirin tashar talabijin ta Channels na sassafe mai suna Morning Brief na yau Talata, yace kudaden daukar nauyin shirin na zuwa ne karkahin shirin samar da lantarki ta hasken rana ga bangaren gwamnati na ma’aikatar lantarki ta tarayyar kasar.
“Sabon shiri ne da aka tsara domin rage tsadar gudanarwa. An ware masa Naira bilyan 100. Za muyi amfani da kudaden wajen samarda da lantarki mai amfani da hasken rana a dukkanin makarantun gwamnati”, a cewarsa.
Dandalin Mu Tattauna