Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Taki Amincewa Da Bukatar Mamu Ta Karbe Ajiyarsa Daga Hannun Hukumar Tsaro Ta DSS


Tukur Mamu
Tukur Mamu

Da yake zartar da hukunci akan batun a yau Litinin, Mai Shari'a Ekwo ya kafa hujja da yawaitar fasa gidajen yari a matsayin dalilin kin amincewa da bukatar mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje.

Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya ki amincewa da bukatar mutumin da ake zargi da zama dan koren 'yan ta’adda, Muhammad Tukur Mamu, ta neman dauke shi daga hannun hukumar tsaro ta DSS zuwa gidan gyaran hali na Kuje

Da yake zartar da hukunci akan batun a yau Litinin, Mai Shari'a Ekwo ya kafa hujja da yawaitar fasa gidajen yari a matsayin dalilin kin amincewa da bukatar mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje.

Mai Shari'a Ekwo ya kara da cewar Mamu bai saba ko yin jayayya da tuhume-tuhumen da doka ta bukaci yayi ba, inda ya cigaba da cewar, kasancewar Mamu bai kalubalanci tuhume-tuhumen ba, yasa aka daukesu a matsayin gaskiya kuma duk zargin daya tabbata gaskiya ne baya bukatar karin tabbatarwa.

Daga bisani alkalin ya bada umarnin Mamu ya cigaba da kasancewa a hannun hukumar tsaro ta DSS tsawon lokacin da zai shafe yana fuskantar tuhumar aikata muggan laifuffuka.

Saidai Mai Shari'a Ekwo ya jaddada umarnin daya bayar tunda fari na kyale Mamu ya gana da likita domin duba lafiyarsa karkashin kulawar Hukumar DSS

A ranar 29 ga watan Afrilu, mamu ta hannun lauyansa, yayi zargin cewar, Hukumar DSS ba ta biyayya ga umarnin da kotun ta bayar na ranar 19 ga watan Disembar daya gabata na kyale shi ya rika ganin likita domin duba lafiyarsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG