Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Maganar Daina Amfani Da Tsoffin Takardun Kudin Naira A Disamba - Ministan Yada Labarai


Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya
Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya

A daidai lokacin da rade-radin daina amfani da tsoffin takardun kudin Naira ya karade kafofin sada zumunta, Ministan yada labaran Najeriya Muhammad Idris, ya ce babu wannan magana.

Ministan yadda labarai da wayar da kan al’umma na Najeriya, Muhammad Idris Malagi, ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da muryar Amurka ta kai ofishinsa da ke birnin tarayya Abuja, a karkashin jagorancin shugaban sashen Hausa Aliyu Mustapha.

A yayin da ake shirin cika shekara daya da kafa mulkin Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, an yi ta yada jita jitar cewa gwamnatin kasar na shirin dakatar da amfani da tsoffin takardun kudin Naira, lamarin da ya sa muryar Amurka ta nemi bayani daga ministan akan ko akwai kamshin gaskiya a batun, amma ministan ya ce sam ba haka bane gwamnati bata da wannan shirin.

Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya
Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya

Da muryar Amurka ta bukaci karin haske a game da lokacin da za’a koma kan batun aiwatar da tsarin karbar harajin tsaron yanar gizo wato Cybersecurity, ministan ya ce ana kan nazari mai zurfi akan lamarin tun bayan dakatar da batun aiwatar da shi.

A game da batun kafa sansanonin sojoji na kasashen waje kamar Amurka da Faransa, Mallam Idris ya bayyana cewa harkar matsalar tsaro ba kasar da zata iya bugar kirji ta ce ita kadai zata iya magance ta, amma duk da haka Najeriya bata da shirin kafa wani sansanin sojin ‘yan kasar waje.

Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya
Ziyarar Muryar Amurka offishin Ministan Yada Labaran Najeriya

Wadannan muhimman batutuwa dai na daga cikin ababen da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya a yayin da ake ganin kasar ta shiga wani yanayin matsi sakamakon irin sabbin manufofin da gwamnatin tarayyar kasar a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta bijiro da su tun bayan karbar ragamar mulki, kama daga cire tallafin Man fetur, da matakin daidaita kasuwannin canjin kudi wanda ya taka rawa wajen karya darajar Naira, da cire tallafin kudin wutar lantarki da dai sauran su.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Babu Maganar Daina Amfani da Tsoffin Takardun Kudi a Disamba - Ministan Yada Labarai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG