Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Gayyaci Shugabannin Tsaro Kan Kisan Gillar Jihar Filato


Zauren Majalisar Dattawan Najeriya.
Zauren Majalisar Dattawan Najeriya.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince cewa kisan gillar da aka yi wa sama da mutane 100 a Filato, a jajibirin Kirsimeti ya faru ne sakamakon gazawar hukumar leken asiri da ta tsaro.

Da take bayyana rashin jin dadin ta, Majalisar Dattawan ta jaddada cewa babban nauyi na farko da tsarin mulki ya rataya a wuyan gwamnati na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, na fuskantar babbar barazana.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana hakan a wani zama na musamman a ranar Asabar din da ta gabata, cewa ta’azzaran kashe-kashen rayuka da ya yawaita a kasa na nuni da gazawar tsaro musamman na bangaren jami’an leken asiri.

Jami’an Majalisar suma cikin muhawara sun nuna matukar bacin ran su da yadda hukumomin tsaro ke ganin cewa ba su da wani taimako kafin kai hare-hare da kuma lokacin hare-haren.

Sakamakon haka, Majalisar Dattawa ta gayyaci shugabannin manyan hukumomin tsaro da suka hada da hafsoshin sojan kasa da na sama, shugaban hafsan tsaron kasa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), darakta-janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sufeto ‘yan sanda, da kuma Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA).

Sanata Diiket Plang ne ya dauki nauyin gabatar da kudirin a yayin zaman, inda ya bayyana cewa an shirya kashe-kashen ne bisa dabara, tare da tanadi makamai a kauyukan da lamarin ya shafa.

Sanata Abdul Ningi, shima ya bayyana binciken da yayi game da kisan gilla da ‘yan ta’adda suka yi a jihar Filato.

Ya ci gaba da bayyana cewa da ya samu labarin faruwar lamarin a lokacin hutun kirsimeti a Bauchi, nan take ya tafi Filato domin tantancewa da idonsa.

Ningi ya bayyana tsananin halin tashin hankali da ake ciki a Bokkos. Ya nanata cewa, "Abin da ya faru a Bokkos ba a taba yin irinsa ba"

A ziyarar da ya kai Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos, ya shaida yadda lamarin ya kasance, inda ya ce, “Na ga jariri dan wata 18 da raunuka na harsashi, wannan abu ya yi matukar muni”

Da yake bayyana bukatar gaggawar samar da ingantaccen hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro, Ningi ya nuna rashin hadin kai a tsakaninsu. Ya jaddada cewa, in har muna son cigaba mai dorewa a kasar nan, dole ne mu baiwa tsaro muhimmanci matuka kuma ya bukaci a dauki matakin gaggawa don magance irin wadannan mummunan al’amura.

“Gwamnatin jihar Filato na cikin tsananin bukata domin a yanzu haka suna da ‘yan gudun hijira a tsugune sama da 150,000, suna ciyar da su.

“dukkanin hukumomin tsaro na jihar sun gaza. Abin da muka gano shi ne, wadannan ’yan fashin ba su zo da makamai ba, a zahiri wadannan makaman suna boye ne a wasu wurare, abin da suke yi shi ne sun zo sun dauke su

“Wannan yana nufin akwai wani abu a bayan abin da ke faruwa a Filato. Su wane ne wadannan kuma a ina suke, domin idan ka je can daga waje za ka dauka yakin addini ne, a’a. Akwai wani abu a bayansa wanda dole ne wannan majalisar dattawa ta warware.

Ningi ya cigaba da cewa "Abin da na kuma gano bayan shafe sa'o'i 72, kadan daga cikin bayanan 'yan fashin, ba sa zaune a cikin al'ummomin. Wani ne ya shigo da su. Wani ne ya raka su.

“Ba su ma san filin ba, wasu mutanen da suka san filin ne suka jagorance su. Kuma idan ka dubi al'ummomi

“Abin da ya faru a jajibirin Kirsimeti wani abu ne da ya kamata hukumomin tsaro su binciki lamarin, kuma bai kamata ya zama kalamai ba. Duk wanda aka ba shi mukamin shugaban tsaro kuma ba zai iya ba, dole a kore shi.” Inji Ningi.

Yanzu dai hankalin ya koma kan shugabannin tsaro da aka gayyace su, inda za su yi wa Majalisar Dattawa bayani kan yadda lamarin mumunar kashe-kashen da ‘yan ta’adda suka yi a jihar Filato.

Majalisar Dattawan dai na da burin daukar mataki na gaba bisa bayanan da shugabannin tsaro zasu bayar.

Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa yanayin yankin da nisan wajan na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas musamman wajen kawo agaji na gaggawa daga bangaren jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa yawaitar kayayyakin tsaro da gwamnatin jihar ke bayarwa ya kamata ya kara musu karfin da za su iya kawo dauki nan take da mayar da martani yadda ya kamata.

Yusuf Aminu Yusif ne ya hada wannan rahotan.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG