ABUJA, NIGERIA - A wani rahoto da ofishin kula da basussuka DMO ya fitar a kwata na biyu na wannan shekara, ya nuna cewa, basussuka wadanda aka ciwo su daga waje da cikin gida, sun kai Naira Triliyan 87.38.
Kuma shi ne karon farko da za a ciwo bashi mai yawa irin wannan, duk da cewa an hada ne da wanda Gwamnatin baya ta ciwo, shi ya sa yawan kudin ya kai Naira Triliyan 87.38.
Wanan lamarin ya dauki hankalin masana tattalin arziki a kasar, inda suka bada shawarwari kan yadda za a sarrafa kudaden idan har ana so a samu nasara wajen tara kudaden shiga masu yawa da za su taimaka wajen biyan basussukan.
Shu'aibu Idris Mikati kwararre a fanin tattalin arziki, ya ce kamata Gwamnati ta san cewa ba ta yi wa ‘yan kasa adalci ba, domin a yanzu yadda kasar Najeriya take, za a ce bashi ya yi mana katutu, wasu daga cikin bashin kasar ma, an kasa biyan kudin ruwa, kuma ga cewa jama'an Najeriya a kusan ko wane lokaci suna kara zama cikin talauci ne.
Mikati ya ce a da mutum ya fi karfin cefane, amma yanzu kuma cefane yana nema ya fi karfin mutum. Mikati ya ce, ya kamata Gwamnati ta samo wa talakawa hanyoyin da za su yi sana'a ko za su mayar da taro ya zama sisi. Ya ce ta nan ne za a iya maganin tashin hankalin da ke addabar mutane, musamman ma a fanin tsaro.
A nashi ra'ayin, masanin tattalin arziki, Yusha’u Aliyu ya yi suka ne da kakkausar murya cewa, wannan bashi zai iya kawo tarnaki a kasafin kudin badi domin wannan bashi, kudi ne mai-yawan gaske, kuma idan an ciwo irin wannan bashi, abu ne mai wahala a iya biyan sa , idan kasa ba ta da hanyoyin samun kudaden shiga. Yusha'u ya ce idan ana so kasar ta samu ci gaba, dole ne a daina cin bashi gaba daya, saboda a yi kokarin biyan wanda ta riga ta ciwo.
Shi kuwa mai nazari kan al'amuran yau da kullum kuma malami a Jami'ar Abuja, Dr. Farouk Bibi Farouk ya yi karin bayani ne cewa, duk lokacin da aka ce bashi ya shiga tsakanin kasashe, dole ne ya zama harka na kasuwanci tsakanin mai bayarwa da mai karba, kuma kuskuren da Najeriya ta ke yi kenan.
Bibi ya ce ana karbo bashin ne ba tare da tsari ba , saboda haka lokacin biya yana zame wa kasar matsala. Bibi ya ce kamata yayi Najeriya ta rika duba abubuwa da za ta yi da kudi kafin ta ciwo bashi, in ba haka ba, ba za ta iya biyan basussukan da ta ke karbowa ba.
Abin jira a gani shi ne irin matakan da Gwamnati za ta dauka wajen bude hanyoyin samun kudaden shiga masu karfi, idan har za a biya wadannan basussuka a cikin lokacin da aka qayyade.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna