Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Dakatar Da Ayyukan Hukumar USAID


  Hukumar Taimaka wa Kasashe na Amurka USAID.
  Hukumar Taimaka wa Kasashe na Amurka USAID.

A ranar Litinin ne aka dakatar da ayyuka a Hukumar Tallafawa Kasashe masu tasowa ta Amurka ta USAID mai gudanar da ayyukan tallafi na biliyoyin dala ga kasashen waje.

A ranar Litinin ne aka dakatar da ayyuka a Hukumar Tallafawa Kasashe masu tasowa ta Amurka ta USAID mai gudanar da ayyukan tallafi na biliyoyin dala ga kasashen waje, inda aka hana ma’aikatan hukumar shiga ofisoshin su sannan an hana su damar amfani da kwamfutocin su. An kuma tilasatawa wasu manyan jami’an hukumar tafiya hutu yayin da gwamnatin Trump ta dau matakan mai da ayyukan hukumar karkashin ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Da yake yiwa manema labarai bayani a El-Salvador, inda ya kai ziyarar aiki, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce yanzu shi ne darektan hukumar na rikon kwarya sannan zai fara daukan matakan da za su tabbatar cewa ayyukan hukumar sun dace da manfofin sabuwar gwamnatin kasar.

Rubio ya bayyana hukumar a matsayin wacce take da tarihin bijirewa umarnin majalisar dokoko da fadar White House, duk da yake, a cewar shi ya kamata ace hukumar tana karkashin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne.

Rubio ya ce, hukumar USAID na yin watsi da hakan, da yanke shawara cewa hakika akwai rarrabewa daga bukatun kasa zuwa taimakawa duniya.

Akwai batun kudin masu biyan haraji, kuma muna da hakkin tabbatarwa al’ummar Amurka duk dalar da za’a kashe a waje, za’a kashe ta ne kan wani lamari da zai daga bukatun kasar mu.

Kalaman na Rubio na da sassauci akan na hamshakin biloniya Elon Musk, wanda shugaba Donald Trump yaba gagarumin karfi don kula da sabuwar hukumar da aka kirkiro da zata kula da ingancin aikin gwamnati(DOGE).

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG