Shugaban Amurka, Donald Trump, jiya Talata, ya janye Amurka daga ayyukan kwamitin hakkin dan Adam a MDD, sannan ya dakatar da tallafi ga hukumar UNRWA mai bada agaji ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira, sannan kuma ya bada umurnin gudanar da bincike a kan ayyukan hukumar da ke kula da wuraren tarihi da al’adu a karkashin MDD, UNESCO.
“Yana da tasiri kuma zamu ci gaba da bada gudunmawar mu bisa tasirin shi amma akwai bukatar su daidaita al’amuransu,” abin da Trump ya fada ma manema labarai kenan. Ya kara da cewa, “Ba a gudanar da hukumar kamar yadda ya kamata, gaskiya, basa ma yin aikin.”
Shugaban na Amurkan y ace “Mu na kokarin ganin cewa mun yi sulhu don kawo karshen yake yaken da ake yi, ko kuma a kalla a ce mun taimaka don ganin sun yi sulhu tsakaninsu. Amma babu taimakon da ake ba mu. Wannan ce babbar manufar MDD.
Kakakin MDD Stephen Dujarric y ace “daga ranar farko, kudaden da Amurka ta ke tallafa wa MDD da su sun taimaka wajen ceto rayukan mutane da dama sannan sun taimaka ma ci gaban da aka samu a fannin tsaro a fadin duniya.”
“Shugaban MDD yana fata cewa dangantakar da ke tsakanin shi da shugaba Donald Trump da gwamnatin Amurka mai ma’ana zat a ci gaba don karfafa wannan dangantakar a duniyarmu ta yau wace ke cike da rudani.”
Trump ya ce ba shi da niyyar karbar kudi daga kungiyar duniyar mai mambobin kasashe 193, ko da yake ya yi korafin cewa gudunmawar da Washington ta ke bayarwa ya fi na kowa.
Washington ne ta ke bada kaso mafi girma a MDD, sannan China kuma take biye da ita, wanda ga baki daya ta ke bada kaso 22% na yawan kudaden kasafin kudin da MDD ta ke kashewa, sannan kuma kaso 27% na yawan kudaden tallafin ayyukan tabbatar da zaman lafiya. MDD ta ce ta na bin Amurka bashin kudi dala biliyan 2.8 wanda dala biliyan 1.5 daga wannan ya kasance na kasafin kudin gudanarwa. Kasashe ba su da zabi akan biyan wadannan kudaden.
Dandalin Mu Tattauna