A yau Juma’a jami’an bada agaji suka bazama neman wani jirgin saman haya daya bata da mutane 10 a cikinsa, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana, a hatsarin jirgin saman Amurka na baya-bayan nan.
An ba da rahoton cewar karamin jirgin saman kirar bering air caravan mai dauke da fasinjoji 9 da matuki daya ya yi jinkiri bayan da ya taso daga Unalakleet zuwa Nome da karfe 4 na yamma agogon Alaska, a cewar rundunar ‘yan sandan Alaska.
Biranen 2 na da tazarar kilomita 235 a tsakaninsu a gabar ruwan Amurka ta yamma.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, hukumar kashe gobarar Nome tace “matukin jirgin ya shaidawa hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewar yana niyar sanya jirgin a tsarin jira yayin da yake jiran titin saukar jiragen ya zama babu komai akai” gabanin bacewarsa.
Dandalin Mu Tattauna