Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Faduwar Kasuwannin Hannayen Jari Sakamakon Hauhawar Kayayyaki A Amurka


Kasuwar Hannayen Jari
Kasuwar Hannayen Jari

Kasuwannin hannayen jari a Amurka sun yi kasa a ranar Juma'a yayin da ake nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyaki da haraji, yayin da wani rahoto da aka sa ido sosai akai ya ba da mabanbancin ma’ana game da kasuwar aikin yi a Amurka.

Kasuwar S&P 500 ya yi kasa da kashi 0.9% kuma fadiwar na kan hanyar share karamar riba ta mako, ana saura sa'a guda ciniki ya tashi. Su ma kasuwannin Dow Jones sun fadi da maki 440, ko 1%. Babbar faduwa ga Amazon biyo bayan labarin riba da ya samu baya-bayan nan da ta taimakawa kamfanin dake zama bangare na kasuwar Nasdaq zuwa ga hasarar kasuwanci mafi girma na 1.4%.

Har ila yau, amfanin bitalmali ya haura a kasuwannin hada-hadar kudi bayan wani rahoto mai karya gwiwa a safiyar Juma'a da ke nuni da cewa ba zato ba tsammani tunanin ana samun bahaguwar fahimta tsakanin masu amfani da kayayyaki a Amurka.

Rahoton farko na Jami'ar Michigan ya ce masu amfani da kayayyaki a Amurka suna sa ran ganin hauhawar farashin kayayyaki a cikin shekara mai zuwa zai kai kashi 4.3%, hasashe mafi girman da aka yi tun 2023.

Wannan shine cikakken ma'aunin kaso sama da abin da suke tsammani a wata guda da ya gabata, kuma shine karo na biyu a jere da aka samu tashin farashi da ba a saba gani ba.

Masana tattalin arziki sun yi nuni da yuwuwar saka haraji da Amurka ke niyar yi kan kayayyaki da dama da ake shigowa da su daga kasashen ketare, wanda shugaba Donald Trump ya gabatar, kuma wanda a karshe zai iya kara tsadar farashi ga masu amfani da kayayyaki a Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG