Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Da Dama Ba Su Ra'ayin Jinkirta Komawar Falasdinawa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.

A jiya Laraba kawayen Amurka da abokan hamayyar ta su ka yi hannun riga da ita kan kudurin shugaba Trump na cewa Amurkan za ta karbe ikon gudanar da yankin Zirin Gaza, da tilasta ma Falasdinawa miliyan 2 komawa wadansu kasashe sannan ya hade yankin da kogin Bahar Rum ya maida shi wurin shakatawa da bude ido na gabar ruwa a yankin gabas ta tsakiya.

Kudurin na Trump, tsohon hamshakin mai harkar saye da sayar da gidaje a birnin NY, ya gamu da martini nan take, inda kusan duniya baki daya ta yi hannun riga da shi, tun bayan da ya gabatar da shi a yayin wani taron manema labarai a fadar White House a ranar Talata, ta re da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Kasashen Birtaniya, China, Jamus, Ireland, Rasha da Spaniya duk sun ce, za su ci gaba da mara baya ga warware lamarin ta samar da kasashe biyu, wato kasar Falasdinu mai cin gashin kanta da za ta hada da Gaza, da yankin Yahudawa 'yan kama wuri zaune na gabar kogin Jordan da ke kusa da Isra’ila.

Hakan na nufin kawo karshen gwamman shekaru na yakin da a ke yi a yankin Gabas Ta Tsakiya, da ya dade da zama kashin bayan manufofin Amurka a yankin, duk da cewa gwamnatin Netanyahu na adawa da hakan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG