Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Gwmanatin Trump Ta Koma Teburin Sulhun Da Zummar Tilasta Ma Falasdinawa Barin Gaza


Trump- Netanyahu 6
Trump- Netanyahu 6

Trump ya ayyana Gaza da “wurin da aka rusa” sannan ya kwatanta batun da sama wa mazauna zirrin Gaza da wani matsuguni a madadin inda suke da yaki ya daidaita.

Shugaban Amurka Donald Trump ya dage akan yunkurin shi na matsa wa Falasdinawa su dan fice daga Gaza, yayin da ya karbi bakoncin Firan Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu a fadar white House a ranar Talata.

“Ya kamata a samo musu wani sabon fili da ba a taba gini a wurin ba mai kyau sannan mu samo mutanen da zasu tara kudi ayi gini sannan a kawata muhallin ya zama gidaje,” abin da Trump ya fada wa manema labarai kenan gabanin ganawar shi da Netanyahu.

Trump ya ayyana Gaza da “wurin da aka rusa” sannan ya kwatanta batun da sama wa mazauna zirin Gaza da wani matsuguni a madadin inda suke da yaki ya daidaita.

“A halin yanzu basu da wani zabi. Me zasu yi? Ya kamata su koma Gaza amma mene ne Gaza?

Ya ce “Babu wani ginin dake tsaye.”

Cikin ‘yan kwanakin nan, dubun dubatan Falasdinawa a yankin kudu maso gabashin Gaza sun dunguma inda gidajen su su ke a yankin arewa bayan da Isra’ila ta bai wa mutane dama umurnin su koma gidajensu kamar yadda sharadin yarjejeniyar tsagaita wuta don sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

A hirar da yayi da manema labarai tun farko a ranar Talata a fadar White House, jakadan Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ya shawarci gwamnati ta duba yiwuwar sake tattaunawa akan wasu sashen yarjejeniyyar tsagaita wutar da aka cimma a ranar 19 ga watan Janairu, wuni 1 gabanin a rantsar da Trump.

“Matsalalar ita ce babu wani abin a yaba a game da yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu ma. Kuma ba gwamnatin Trump ce ta bada umarnin a yi hakan ba. Babu ruwanmu da shi,” inji Wattkins. “Yanzu mu na kokarin yin abin da ya sawwaka don samun mafita.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG