A ranar Litinin a ofishinsa na Oval Trump ya ce, suna kyautata zaton kulla wata yarjejeniya da Ukraine inda za a yi bani gishirin in baka manda da arzikin albarkatun karkashin kasa da Allah ya huwacewa kasar da sauran su.
Trump ya nusar da alamun amincewar Ukraine ga yarjejeniyar ta samar da albarkatun kasar ga Amurka domin samun cigaba da tallafi daga Amurkan a yakin da take yi da Rasha, cewar wani rahoton kafar labarun Associated Press.
Shugaban Amurkan ya kara da cewa, za su sa daruruwan biliyoyin dala akan Shirin. Ukraine da muhimman albarkatun karkashin kasa, kuma a shirye suke su yi hakan.
Irin wadannan muhimman albarkatun karkashin kasa dake Ukraine sun hada da Lithium da titanium. Ma’adanai ne dake da muhimmancin gaske a jerin manyan kayayyakin na’urorin zamani.
A jawabin da yake yi a duk rana, a ranar Litinin, kafin sanarwar ta shugaba Trump, shugaban Ukraine ya jaddada bukatar da kasar ke da shi na kare kanta daga cigaba da hare haren Rasha. Ya ce, musamman Rasha na maida hankali kan kullatar bangaren makamashin Ukraine.
Volodymyr Zelensky ya kara da cewa, Rasha na cigaba da kai hare hare akai akai, inda suke sauya akalar hare haren kan bangaren tsaron Ukraine, da hakan keda wahalar tunkara.
Shugaba Trump ya ce, ana samun sauyi cikin sauri kan yadda ake gudanar da yake yake da na’urori masu amfani da lantarki, don haka ya bukaci Ukraine da ta kara aza kaimi domin sajewa da canje canjen dake wanzuwa.
Zelensky ya ce, samar da na’urorin tsaron sararin samaniya ga Ukraine wani batu ne ga kasashen gabahin Turai, da samar dasu keda muhimmanci gaske ga Ukraine da ko da wasa bai kamata a dakata ba.
Hakazalika Zelensky ya yi magana a jawabin na shi na kullum kullum a ranar Litinin tare da kwamandan dakarun Ukraine Oleksandr Syrskyi game da zamanantar da rundunar dakarun kasar.
Dandalin Mu Tattauna