Shugaban ya yi wadannan kalamai ne yayin da shi da Firai Ministan Japan Shigeru Ishiba wanda ke ziyara suke ganawa da manema labarai a fadar White House kafin shugabannin biyu suka shiga tattaunawa.
Da yake amsa tambaya da aka masa game da shawararsa kan Gaza, Trump ya ce shawararsa ta samu karbuwa sosai, kuma kamar yanda yasa rai, Amurka bata bukatar jibge dakaru kasa a yankin, saboda Isra’ila zata bada tsaro. Ya ce yana tunanin babu wani saka hannun jari daga Amurka "koma wani abu."
A farkon makon nan ne Trump ya sanar da shirinsa na karbar Gaza yayin da yake tare da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a wani taron manema labarai a fadar White House. Daga baya Trump ya ba da karin bayani kan shirin a dandalinsa na True Social, yana mai ba da shawarar Isra'ila ta mayar da Zirin Gaza ga Amurka bayan yakinta da Hamas ya kare.
A karkashin shirin nasa, ya ce, da an riga an sake tsugunar da Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke zaune a wurin a cikin yanayi mafi aminci da unguwanni masu tsari.
A wata sanarwar faifan bidiyo a ranar Alhamis, yayin ziyararsa a Washington, Netanyahu ya yabawa Shirin, yana mai cewa batun nada dadin sauraro, kuma karo na farko kenan a cikin shekaru da aka kawo shawara mai ma'ana.
Kawayen Amurka da abokan gaba sun yi ta nuna damuwa sosai kan shirin, wadanda da yawa daga cikinsu suka jajirce wajen samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu tare da Isra’ila, wanda aka fi sani da “matsalar kasashe biyu.”
An gudanar da wata gagarumar zanga-zangar adawa da shirin a birnin Amman na kasar Jordan a ranar Juma'a. A wajen zanga-zangar da kungiyar 'yan uwa Musulmi da sauran jam'iyyun adawa suka shirya, masu tattakin suna dauke da kwalaye da kyelle masu rubutun dake Allah wadai da Trump da kuma rera taken goyon bayan Falasdinawa.
Dandalin Mu Tattauna