A jiya talata Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan umarnin zartarwar da ya janye Washington daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da dama, ciki har da kwamitin kare hakkin dan adam (UNHRC) tare da fadada nazari a kan kudaden da Amurka ke kashe wa majalisar.
Umarnin zartarwar ya bayyana janyewar Washington daga UNHRC da babbar hukumar bada agaji ta majalisar akan Falasdinawa (UNRWA), sannan zata sake nazari akan rawar da take takawa a hukumar raya ilmi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).
An dauki matakin ne domin nuna adawa da abin da sakataren ma'aikatan fadar White House Will Scharf ya bayyana da dabi'un kyamar Amurka a hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Ga alama umarnin zartarwar zai kawo karshen rawar da Amurka ke takawa a ayyukan majalisar, da suka hada da nazartar bayanan tarihin kare hakkin dan adam a kasashe da kuma kebabbun zarge-zargen tauye hakkin dan adam.
"Gaba-daya dai, umarnin zartarwar na neman ayi gyara a kan rawar da Amurka ke takawa da daukar nauyin Majalisar Dinkin Duniya duba da katafaren bambancin da ke akwai a matakan daukar nauyin majalisar a tsakanin mabambantan kasashe," a cewar Scharf.
Trump ya bayyana "katafaren mUhimmancin da majalisar ke da shi sai dai yace ba'a gudanar da shi yadda ya dace."
Dandalin Mu Tattauna