Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawa Kan Kudirin Kashe Kudin Gwamnatin Amurka Na Fuskantar Cikas


State of the Union
State of the Union

Shugabannin Republican da na Democrat a kwamitocin kasafin kudi guda biyu a Majalisa sun gudanar da tattaunawa kan kudirin kashe kudin gwamnati a karshen watan Janairu, hadimai sun ce bangarorin biyu sun kuduri aniyar cimma matsaya. Sai dai fatan alheri yana dushewa a 'yan kwanakin nan.

Kafin Shugaba Donald Trump da 'yan Republican a Majalisa su zartar da mafi yawan ajandarsu a majalisu dokokin kasar, dole ne su tunkari wasu harkokin da ba a kammala ba, kamar karasa aiki kan kudirin kashe kudi na wannan shekarar. Aiki ne wanda bisa ga dukkan alamu baya tafiya da kyau.

Matakin wucin gadi a yanzu na warwaren batun kasafin kudi yana ci gaba da kasancewa har izuwa ranar 14 ga Maris. Bayan haka, idan majalisa bata dauki wani mataki ba, za a rufe wani bangare na aikin gwamnati.

Makonni biyar tamkar shekaru aru-aru ne wurin warware batun kudirin kashe kudi a Washington. Sai dai makonnin farko da Trump ya yi a kan karagar mulki sun kara ta’azzara tankiya tsakanin bangarorin biyu yayin da sabuwar gwamnatin ke sake fasalin wasu muhimman ayyukan hukumar tare da wargaza shirye-shiryen da ake da su ba tare da amincewar majalisa ba.

Shugabannin Republican da na Democrat a kwamitocin kasafin kudi guda biyu a Majalisa sun gudanar da tattaunawa kan kudirin kashe kudi a karshen watan Janairu, hadimai sun ce bangarorin biyu sun kuduri aniyar cimma matsaya. Sai dai fatan alheri ya dushe a 'yan kwanakin nan.

"Tabbas, 'yan jam'iyyar Democrat ba su da matsaya mai kyau a yanzu, don haka sun fice daga tattaunawar. Amma dole ne a koma a ci gaba," in ji shugaban masu rinjaye a majalisar Steve Scalise, dan Republican daga Louisiana, a ranar Alhamis.

Kakakin majalisar Mike Johnson, dan Republican daga Louisiana, ya ba da irin wannan bayani, yana mai cewa kalaman shugaban jam'iyyar Democrat Hakeem Jeffries na New York da wasu abokan aikinsa sun nuna alamun suna "kokarin daukar wani mataki na rufe wasu ayyukan gwamnati, wanda ina ganin abin takaici ne sosai.

Mun kasance muna tattaunawa da gaskiya kuma muna kokarin samun nasara, amma kamar yadda na sani, sun kasance ba su ba da hadin kai a cikin kwanakin biyun da suka gabata. Don haka ina fata za mu sake komawa ga tattaunawar."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG