Babu wani rata mai yawa tsakanin inda Ceci Carroll take zama, wani kamfanin fasa duwatsu da ya gurbata iska da kurar da ke tashi a fadin kwarin San Gabriel.
Yanzu da ma’aikata suke kokarin kwashe tarkace daga wuraren da suka kone a gobarar daji a Los Angeles, Carroll tana fargaba akan wata sabuwar matsalar gurbacewar muhalli; wani fili inda ake sarrafa tarkacen gidajen da suka kone a gobarar daji a Eaton.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, Carroll wacce ta shafe shekaru 23, a Duarte ta ce “Ina fargaba akan halin da al’ummar take ciki da kuma makarantun da suke wannan yankin, inda yaran mu suke zuwa”.
“Mun damu akan wurin da ake saraffa sinadarai da abubuwa masu illa (guba) ta ce. “Iyaye sun damu sossai”.
Carroll ta kasance cikin mazauna Duarte, Azusa da biranen da ke kewaye da basu amince da matakin da Hukumar kare Muhalli ta dauka ba, na yin amfani da filin shakatawa na Lario Park a Irwindale a matsayin wurin da zata tattara tarkacen kayayakin da suka kone a gobarar Eaton masu sinadarai masu cutarwa.
A lokacin da muke zaune kalau, mutane suna zuwa shakatawa, suna tuka keke ko hawan dawakai a wuraren da aka kebe don hawan dawakai a filin dake zama mallakin gwamnatin tarayya. Yanzu hankalin su ya tashi akan tarkacen mai guba da zai iya gurbata iskar da suke shaka ko kuma ya bi hanyar ruwa a cikin kasa.
Gobarar da ta fara ruruwa a ranar 7 ga watan Janairu ta kone dubban gidaje, motoci da kayan laturoni a fadin yankin Los Angeles. Hukumar kare muhallin ta fara aiki haikan don kawar da daruruwan ton din tarkacen dake dauke da sinadarai masu guba daga gobarar dajin Eaton da Palisades. Wandanda suka hada da fenti, maganin kwari, sinadarai masu narka fenti, tukwanen iskar gas, albarussai da batiran motoci masu sinadaren Litium-ion da ka iya cutarwa idan suka kone.
“Bai kamata ace kwashe tarkacen nan ya gurbata muhallin al’ummar da take fama da mummunar tasirin gubatacen yanayi ba,” a cewar na’ibar shugaban hukumar yankin Los Angeles Hilda Solis cikin wata sanarwa.
Bayanan ofishin Hukumar dake Hasashen lafiyar Muhalli sun nuna cewa, al’ummomin Latino dake daura da filin sun fi kasancewa cikin hadarin fuskantar matsalar sinadarai masu keta rufin sararin samaniya da gurbatacen sinadarai da ke yawo a iska da ake kira particulate matter da harshen turanci fiye da wuk wani yanki.
Kwararru sun tabbatar da fargabar da mazauna yankin suke bayyanawa, amma sun ce ba lallai ne ya kasance cewa tarkace mai guba zai cutar ba, muddin aka kiyaye matakan kariya sannan ba za a bar tarkace mai guban a wurin tsawon shekaru ba.
Dandalin Mu Tattauna