Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marigayi Jimmy Carter Ya Lashe Lambar Yabon Grammy Bayan Rasuwar Shi


FILE - Former President Jimmy Carter teaches Sunday School class at Maranatha Baptist Church in his hometown of Plains, Georgia, Aug. 23, 2015. Audio recordings from his classes just earned the late president a Grammy.
FILE - Former President Jimmy Carter teaches Sunday School class at Maranatha Baptist Church in his hometown of Plains, Georgia, Aug. 23, 2015. Audio recordings from his classes just earned the late president a Grammy.

Marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, manomin gaydar da ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan rikicin Watergate da yakin Vietnam ya mutu a watan Disamban 2024 yana da shekaru 100 a duniya.

Kafin mutuwar shi, an zabi Carter a jerin wadanda suka yi ayyukan da suka birge a rukunin littattafai cikin sauti, karatu da labari cikin sauti na kyautar Grammy na 2025 akan littafinsa mai taken “Last Sundays In Plains”: Wanda ya kunshi labarin shi na bukin cika shekaru 100,” da ya kunshi sautin muryar shi ta karshe na darussan da yake koyarwa na Sunday School a majami’ar Maranatha Baptist Church dake jihar Georgia.

Muryoyin mawaka irin su Darius Rucker, Lee Ann Rimes da Jon Batists sun kasance a cikin wannan sautin.

Wannan shine kyautar Grammy na 4 da Carter ya samu. Wannan kyautar da ya samu bayan mutuwar shi ya biyo bayan wasu kyautatuka 3 da ya samu a rukunin adabin baka.

Da tsohon shugaban ya lashe wannan kyautar kafin ya mutu, da ya kasance wanda ya lashe kyautar Grammy mafi yawan shekaru a tarihi.

Jikan Jimmy Carter Jason Carter, ne ya karbi kyautar a madadin shi. “Sarrafa (yin amfani) da kalmomin shi ta wannan hanyar abin a yaba ne ga iyalen shi da ma duniya baki daya,” abin da ya fada kenan a sa’adda yake gabatar da jawabin amincewa (godiya). “Ina godiya ga masanana”.

A wannan rukunin, Jimmy Carter ya doke Barbra Streisand, George Clinton, Dolly Parton da Frodusa Guy Oldfield.

Da a ce Streisand ce ta lashe kyautar ba Carter ba, da wannan ya kasance karon farko da ta taba lashe kyautar Grammy cikin shekaru 38.

A halin yanzu dai, mutumin da ya lashe kyautar ta Grammy da ya fi yawan shekaru a 2011 shine Pinetop Perkins mai shekaru 97.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG