Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Baiwa Musk Umurnin Rufe Hukumar Raya Kasashe Ta Amurka, USAID


Hakan na zuwa ne bayan da Musk, wanda ke jagorantar aikin yiwa tsarin gwamnatin tarayyar Amurka garanbawul (DOGE) ya bayyana da safiyar yau Litinin cewa ya zanta da Trump kan hukumar raya kasashen ta Amurka mai shekaru 60 kuma ya amince mu rufeta.”

A yau Litinin, an umarci ilahirin ma’aikatan hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) da su kauracewa shelkwatarta dake birnin Washingto, kamar yadda sanarwar da aka rarraba musu ta bayyana, bayan da attajiri Elon Musk ya sanar da cewa Shugaba Donald Trump ya amince da shi a kan rufe hukumar.

Ma’aikatan USAID sun ce suna bin diddigin fiye da ma’aikata 600 da suka bada rahoton cewar an wayi gari an katsesu daga shiga tsarin komfutocin hukumar. Wadanda suka kasance a cikin tsarin kuwa sun samu sakonnin emel dake cewar a bisa umarnin jagorancin hukumar za’a hana ma’aikata shiga ginin shelkwatar hukumar a ranar Litinin 3 ga watan Febrairun da muke ciki.”

Hakan na zuwa ne bayan da Musk, wanda ke jagorantar aikin yiwa tsarin gwamnatin tarayyar Amurka garanbawul (DOGE) ya bayyana da safiyar yau Litinin cewa ya zanta da Trump kan hukumar raya kasashen ta Amurka mai shekaru 60 kuma ya amince mu rufeta.”

“Ya bayyana cewarhukumar tamkar kitso ne da kwarkwata,” a cewar Musk a bayanin da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar yau Litinin. Abinda yake gaban jagwalgwalo ne. Ya zama wajibi mu watsar da komai. domin ba zai gyaru ba.”

“Rufeta zamu yi,” a cewarsa.

Musk da Trump da wasu ‘ya‘yan jam’iiyar Republican dake Majalisar Dokokin Kasar na caccakar hukumar raya kasashen wacce ke kula da ayyuakan bada agaji da tsare-tsaren raya kasa da tsaro a wasu kasashe 120, da kausasan kalamai, inda suke zarginta da dabbaka akidun baiwa kowa ‘yanci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG