Shugaban Amurka Donald Trump ya fadada yakin da yake yi da abokan cinikayyarsa a jiya Talata, inda yayi barazanar kakaba harajin kaso 25 cikin 100 akan motocin da ake shigarwa kasar da kara makamancin harajin akan magunguna da sinadaran da ake amfani dasu wajen kera na’urori irinsu komfuta da wayar hannu da dangoginsu.
Trump ya sanar da jerin harajin akan wasu daga cikin manyan abokan cinikayyar Amurka tun bayan daya dare kan mulki a watan Janairun da ya gabata, inda yace hakan zai magance zamba a kasuwanci-wasu lokutanma za’a iya amfani da barazanar wajen janyo sauyin manufa.
A baya-bayan nan ya sha alwashin dora harajin kaso 10 cikin 100 a dukkanin kayayyakin da ake shigarwa Amurka daga China, sannan kaso 25 akan kayayyakin karafa da gorar ruwa da aka shigo da su.
A wurin shakatawarsa na Mar-A-Lago dake Florida, Trump ya shaidawa manema labarai cewar harajin da za’a dorawa bangaren motocin zai kai kimanin kaso 25 cikin 100,” inda za’a fayyace hakan a ranar 2 ga watan Afrilu mai zuwa.
Da aka tambaye shi game da barazanar kakaba harajin da yayi a bangaren magunguna da na’urorin harhada komfuta, trump yace: “zasu kasance kaso 25 cikin 100 koma su dara, sannan zasu cigaba da karuwa kafin shekarar ta kare.”
Dandalin Mu Tattauna