Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana da kakkausan lafazi akan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, a jiya Laraba, inda ya kira shi da dan kama karya, da ya gaza gudanar da zabe, bayan da Zelenskyy ya zargi Trump din da biye wa shaci fadin Rasha.
A yayin da sasanci kan shekaru ukun da Rasha ta kwashe tana yaki da Ukraine ke tangal tangal, Trump ya garzaya shafinsa a kafar sada zumuntar shi na Truth Social inda ya soki shugaban na Ukraine, wanda tuni ya bayyana tsoron cewa, shugaban Amurkan na kokarin kawo karshen yakin bisa sharuddan da suka yi wa Moscow dadi sabanin Kyiv.
Trump ya zargi Zelenskyy da kin gudanar da zabe a Ukraine, wanda aka shirya yi a watan Afirilun shekarar 2024, amma aka jinkirta bayan da Rasha ta mamaye kasar a shekarar 2022, da zai cika shekaru 3 da wucewa a mako mai zuwa.
Trump ya zolayi Zelenskyy inda ya kira shi da dan wasan barkwanci mai mutunci da ya samu nasara, wanda ya ja Amurka ta kashe kudi dala biliyan 350 da shiga yakin da ba za a iya yin nasara a cikin shi ba, da tun farko ma bai kamata a soma shi ba, ya ce, amma kuma yaki ne da in bacin Amurka da shi Trump kan shi, da ba wanda yasan ranar kare shi.
Dandalin Mu Tattauna